Martanin kasashen duniya kan kudirin Trump na kwashe Falasdinawa da karfin tsiya daga Gaza.
Kalaman tsokanar da shugaban Amurka ya yi dangane da tilastawa Falasdinawan kaura daga Gaza ya janyo cece-ku-ce, kuma mutanen Gaza sun yi watsi da qudurin na Trump.
Kungiyar Hamas ta yi watsi da qudurin Donald Trump a fili dangane da tilastawa Falasdinawa kauracewa gidajensu, inda tace za a ba wa gwamnatin sahyoniyawan lada a maimakon a yi musu shari'a kan laifin kisan kare dangi a Gaza da suka yi.
Kungiyar Hamas ta yi kira ga kasashen Larabawa da Musulunci da kuma kasa da su tsaya tsayin daka don tallafawa hakkin al'ummar Palasdinu na kafa kasarsu da birnin Kudus zai zama matsayin babban birninta.
Hamas ta kuma yi kira ga Trump da ya janye kalaman nasa, wadanda suka saba wa dokokin kasa da kasa.
Sami Abu Zuhri, wani jigo a kungiyar, ya yi watsi da kalaman Trump, yana mai kiransu da cewa qudiri ne da zai haifar da rikici da tashin hankali a yankin.
Ya jaddada cewa al'ummar Palasdinu ba za su amince a aiwatar da qudurin Trump ba, kuma abin da ya kamata a yi a aikace shi ne kawo karshen mamayar da ake yi a Gaza da kuma korar jama'arsu daga yankunansu.
Kakakin Hamas Hazem Qassem ya kuma yi watsi da kalaman wariyar launin fata na Trump, ya kuma jaddada cewa za a iya aiwatar da aikin sake gina Gaza da kasancewar mutanenta a cikin ta, ba tare da raba mazaunanta da gidajensu ba.
Izzatur-Rishq, daya daga cikin manyan jami'an Hamas, ya ce a nasa bangaren, kalaman na Trump wani yunkuri ne na ruguza al'ummar Palastinu, kuma al'ummar Gaza ba za su amince da duk wata shawara ta kawar da su daga kasarsu ba.
A nasa bangaren, jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya ce tilas ne shugabannin duniya da kasashen duniya su mutunta ra'ayin Falasdinawa da kuma burinsu na ci gaba da kasancewa a Gaza.
Dangane da shawarar da Trump ya gabatar, kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu, yayin da take yin kakkausar suka kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na kauratar da al'ummar Gaza, ta sanar da cewa watanni 15 gwamnatin sahyoniyawa ta ɗauka tana ta'addanci da makaman Amurka akan gaza, amma basu sanya al'ummar Gaza yin hijira ba.
Kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu ta dauki shawarar shugaban Amurka a matsayin wani sabon salo shelar Balfour ce.
Sheikh Ikrimah Sabri, mai wa'azin masallacin Al-Aqsa, ya ce yayin da yake mayar da martani ga kalaman Trump na korar Falasdinawa daga kasarsu: "Za mu tabbata a kan matsayinmu, ko da kuwa ya kai mu ga biyan zo farashi mai tsada". "Ya zama wajibi a kan kasashen dake makwabtaka da su su bijirewa wadannan matsin lamba kuma kada su mika wuya ga matsin lambar Amurka".
A martaninsa ga Donald Trump kan batun da ya yi dangane da mamayar Gaza da kuma korar Falasdinawa, Mahmoud Abbas shugaban hukumar Palasdinawa ya jaddada cewa: "Mun yi watsi da duk wani shiri na mamaye zirin Gaza da kuma tilastawa al'ummar Palasdinu kaura".
Riyadh ta jaddada matsayar ta ta hanyar yin watsi da rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters da ya ambato Trump na cewa Saudiyya ba ta son kafa kasar Falasdinu.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar da cewa matsayinta na kafa kasar Falasdinu ba abu ne da zai yi girgiɗi ba yana nan daram, sannan kuma ta yi kakkausar suka kan take hakkin al'ummar Palastinu, da suka hada da gina matsuguni, mamaye filayen Palasdinawa, ko kuma korar al'ummar Palasdinu daga yankunansu.
Sanarwar ta ce, yarima mai jiran gado na Saudiyya ya kuma jaddada wannan matsayi a cikin jawabansa a bayyane, kuma ba za a iya jirkita shi ba, yana mai cewa: Saudiyya ba za ta daina kokarin wajen kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta tare da gabashin birnin Kudus a matsayin babban birninta ba, kuma Saudiyya ba za ta kulla huldar jakadanci da Isra'ila ba idan ba aiwatar da hakan ba.
Muhammad Ali Al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasar kasar Yemen, ya bayyana kalaman na Trump a matsayin rashin kunya da tsokana, ya kuma yi kira da a dauki matsaya na gaba daya a kai.
Firaministan Ostireliya ya kuma sanar da cewa, matsayin kasarsa kan Gaza bai canja ba, bayan da Trump ya bayyana shirinsa na mamaye zirin Gaza, kuma Canberra na goyon bayan samar da kasashe biyu.
Wakilan Amurka Chris Murphy da Jake Auchinclas sun bayyana cewa, Trump ya fita hankalinsa kwata-kwata; Domin shawarar tasa za ta iya hana aiwatar da kashi na biyu na tsagaita wutar.
Sanatocin biyu sun yi gargadin cewa harin da Amurka za ta kai a Gaza zai haifar da mutuwar dubban sojojin Amurka da kuma yakin da aka shafe shekaru da dama ana yi a Gabas ta Tsakiya.
Ministan harkokin wajen Jamus ya ce dangane da haka: Gaza ta Falasdinawa ce.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce "Shawarar da Trump ya bayar na gudanarwa kan zirin Gaza abin mamaki ne matuka".
Ma'aikatar harkokin wajen Indonesiya ta bayyana cewa: "Mun yi watsi da duk wani yunkuri na tilastawa Falasdinawa yin hijira ko kuma sauya fasalin yankunan Falasdinawa da aka mamaye".
Dangane da haka, ministan harkokin wajen Spain ya ce: "Mun yi watsi da shawarar da Trump ya bayar na sake tsugunar da Falasdinawa a wasu wurare da kuma iko da Gaza domin samar da "Riviera ta Gabas ta Tsakiya" (yankin yawon bude ido na Gabas ta Tsakiya).
Firaministan Birtaniya ya jaddada cewa: Dole ne a bar Falasdinawa su koma yankunansu sannan kuma a fara aikin sake gina kasar.
Gwamnatin Taliban ta kuma dauki kalaman Trump game da korar mazauna Gaza a matsayin keta dokokin kasa da kasa.
Ministan harkokin wajen Cuba ya ce: Gaza ta al'ummar Palasdinu ce, kuma wajibi ne Isra'ila da Amurka su mutunta wannan.
Ministan harkokin wajen Turkiyya ya kuma dauki matakin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ba abu ne da zai samu karɓuwa ga kasashen yankin da Turkiyya ba ne.
Firaministan Scotland ya bayyana cewa: Duk wata shawara ta korar Falasdinawa daga yankunansu abu ne mai hadari kuma ba za a amince da shi ba.
Ma'aikatar harkokin wajen Masar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: "Muna jaddada matsayinmu na a aiwatar da shirye-shiryen sake gina Gaza ba tare da bukatar tilastawa Falasdinawa kaura daga wannan yanki ba".
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da cewa: "Korar tilasta ga mutanen Gaza ya zama sabawa dokokin kasa da kasa ne".
Ma'aikatar harkokin wajen Oman ta jaddada cewa: "Muna jaddada matsayin kasar Oman tare na kin amincewa da duk wani yunkuri na korar mazauna Gaza da kuma yankunan Falasdinu".
Wakilin kasar Sin a komitin sulhun ya bayyana cewa: Sin na adawa da duk wani yunkuri na sauya ginin al'ummar yankunan Falasdinu da aka mamaye. "Maganganun da Trump ya yi game da Gaza ba su da wata ma'ana, kuma kasashen Larabawa sun yi watsi da shawarar Trump".
A mayar da martani ga kalaman Trump, ma'aikatar harkokin wajen Belgium ta ce: zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya yana bukatar cikakken mutunta dokokin kasa da kasa da aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu. "Muna goyon bayan shiga tsakani na Amurka, Qatar, da Masar da nufin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza".
